Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Gui?i

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Alhamis, goma sha tara ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyar ga watan Nuwamba, shekarar 2020.

  1. Jiya Ministoci suka soma yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bayani a kan aikin da ya tura kowannensu wajen mutanensa su tattaro, barnar da ta auku sakamakon zanga-zangar #ENDSARS. Fashola ya masa bayanin Legas.
  2. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 155 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 85
Abuja 23
Ondo 18
Ogun 8
Kaduna 5
Oyo 5
Taraba 5
Kano 3
Ribas 2
Binuwai 1

Jimillar da suka harbu 63,328
Jimillar da suka warke 59,675
Jimillar da ke jinya 2,498
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,155

  1. An sake darewa teburin sasantawa tsakanin Gwamnatin Tarayya, da Kungiyar Malaman Jami’o’i ko a samu malaman su koma aji. Bayanai na baya-bayan nan na nuna an tashi taron baram-baram.
  2. Hukumar Zabe Ta Kasa INEC, ta ce a watanni uku na farkon shekara mai zuwa, za ta soma rajistar masu zabe.
  3. Gwamnatin Jihar Kaduna ta cire dokar hana walwala da ta sa, daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe a duka kananan hukumomi 23 da ke jihar.
  4. Kidinafas sun harbe wata matar aure Aisha, mai tsohon ciki da ‘ya’ya uku, shekaranjiya cikin dare, a gidan mijinta da ke Rigachikun ta jihar Kaduna. Sun harbeta ta rasu.
  5. Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC a takaice, za ta gudanar da bincike a kan zargin kashe-kashe da ake zargin jami’an tsaro sun yi wa masu zanga-zanga.
  6. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi. Wasu ma’aikatan cibiyoyin ilimi har yanzun ba su ga dilin-dilin na watan jiya ba.
  7. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya duk da alkawarin da ake ta musu. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da Shugaban Karamar Hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, cewa idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  8. Donald Trump ya hango alamun mulkin Amurka zai subuce masa zuwa hannun Biden, ya ce zai garzaya kotun koli. Ya ma ce shi ya yi nasara alhali ba a kammala kidayar kuri’un da aka kada ba. Bayanai na baya-bayan nan na nuna Joe Biden ya lashe zaben.

Mu wayi gari lafiya.

Af!

Matasan Arewa sun mayar wa da Gwamnonin jihohin Arewa da Sarakuna da sauran jiga-jigai da kusoshin Arewa da suka taru a Kaduna, suke batun mara wa shugaban kasa baya a kan dokar hana walwala a soshiyal midiya martani. Suka ce abin da kunya, a daidai lokacin da gwamnonin kudu da duk wasu manyansu, suka dukufa ga neman a biya mutanensu diyya, da kururuwa an kashe musu jama’a a Lekki don duniya ta ji, su na Arewa na magana ne a kan soshiyal midiya. Matasan suka ce an kashe mutanen Arewa a jihohin Inyamurai, da lalata musu dukiya har da masallatai, manyan na Arewa sun yi tsit a kai, ba su ta da wasu wakilai na musamman su je can su tantance barnar da aka yi wa mutanen Arewa ba. Ko su ma je da kansu ba sako ba. Soshiyal Midiya ce ta dame su.
Matasan suka ce, kullum matsalar kidinafin, da satar dabbobi, da lalata dukiya, da kashe rayuka, ga fatara, duk sun dabaibaye Arewa, ba su ne a gaban gwamnoni da ministocin Arewa ba, soshiyal midiya ce a gabansu. Suka ce Allah Ya wadaran naka ya lalace, wai rakumin dawa da ya ga na gida.
Suka ce abin da ya fi damun gwamnonin Arewa shi ne yadda za a kasa kudi a Abuja kowanne ya kwashi rabonsa ya yi gaba. Duk wani batu da suke yi a kan tsaro a Arewa, da fatar baki ne. Matasan sun yi wadannan korafe-korafen ne a wani taro na manena labaru a nan Kaduna.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Related posts

Leave a Comment