Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Gui?i

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Talata, goma ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da bakwai ga watan Oktoba, shekarar 2020.

  1. Gwamnatin tarayya ta ce ba ta ce sai wani gwamna ya jira, ta ba shi izini kafin ya raba kayan tallafi na kwaronabairos ba. Ita kuma Zahra Buhari ta ce ta gode wa Allah da aka yi wallakiya aka gane ba mahaifinta ne matsalar kasar nan ba. Rijiya na bayarwa guga ke hanawa. Kodayake gwamnatin tarayya ta bayyana kayan abincin da ake ta gani a sito-sito ana wawasonsu, ba wanda ta bayar ba ne. Tallafi ne da gamayyar kungiyoyin ‘yan kasuwa da sauran masu hali suka yi karo-karo suka tanadar don a raba wa jama’a saboda kwaronabairos.
  2. Mataimakin Shugaban kasa Osinbanjo ya jagoranci taron majalisar koli ta tattalin arzikin kasar nan, har suka kafa kwamitin da zai lalubo yadda za a tallafawa tattalin arzikin matasan Nijeriya.
  3. Ministan lantarki ya ce kwanan nan za a samar wa miliyoyin matasan Nijeriya aikin yi bangaren lantarki. Ya ce akwai aikin sanya wuta mai aiki da hasken rana guda miliyan dari biyar. Ga aikin sanya wa gidaje da sauransu mitar-iya-kudinka-iya-shagalinka, aikin da duk matasa za a dauka su yi.
  4. Kidinafas sun leka kauyen Lingyado, da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, suka yi kidinafin Hakimi da wasu mutum hudu.
  5. Ana ci gaba da balle sito-sito na abinci da sauran kayan tallafi a sassan kasar nan, ana kuma kama masu wawason. A Abuja an kama mutum 51, a Kwara an kama mutum 144 da sauransu. An balle sito-sito na jihar Kogi, da kuma wasu a Gwagwalada.
  6. Janar Tukur Buratai ya hori manyan sojojin kasar nan, kada su yarda ko da wasu su kyale wani ko da kuwa giyar wake ya sha, ya kai wa sansanin soja ko wani bangare na soja hari ya sha. Ya ce ya gano wasu na son durkusar da kasar shi ya sa har suke iya mamaya su saci makamai da sunan :#ENDSARS.
  7. Kungiyar kare hakki ta SERAP ta ce za ta kai hukumar gidajen rediyo da talabijin ta kasa NBC kara kotu,, saboda cin tarar tasoshin talabijin na Channels, da AIT, da Arise da ta yi. Haka nan kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ ta nuna rashin jin dadinta a kan wannan cin tara, da cewa rashin mutunci ne ga kafofin watsa labaru.
  8. Gwamnatin jihar Kaduna ta dage dokar hana walwala da ta sa a fadin jihar Kaduna, in ban da karamar hukumar Chikun da ta Kaduna ta Kudu. Sauran wuraren da aka sakar wa jama’a mara za su fita karfe shida na safiyar nan, zuwa karfe hudu na la’asar kowa ya san inda dare ya masa. Sai dai mu misali Kinkinau, da su Tudun Wada,, da Sabon Gari, zuwa Sanusi da Badikko da Mu’azu da Tudun Nufawa da ba mu taba kayan kowa ba, kuma muna karamar hukumar Kaduna ta kudu da aka hana fita, ya za a yi?
  9. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba hanya. Gadar da sukan samu su haura ta balle. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  10. Idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, za su cika shekara biyu suna zaman dakon ariyas na sabon albashi.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya wasu na ta tambayar kwaronabairos don da alama kasuwar ta dawo. Ina kuwa leka dandalin da ake cin kasuwar sai na ga an yanka alkaluman shekaranjiya da na jiya kamar haka:

Shekaranjiya akwai sabbin harbuwa 62 kamar haka:

Taraba 18
Ogun 15
Abuja 6
Kaduna 6
Katsina 4
Ondo 4
Ekiti 3
Ribas 3
Kano 1
Ogun 1
Sakkwato 1
Jimillar da suka harbu 61,992
Jimillar da suka warke 57,465
Jimillar da ke jinya 3,397
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,130

Wadanda suka harbu jiya kuwa 199 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 77
Abuja 26
Filato 9
Edo 4
Oyo 2
Nasarawa 1
Jimillar da suka harbu 62,111
Jimillar da suka warke 57,571
Jimillar da ke jinya 3,408
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,132

Kare da ya ga rawar kura ya ce da kyau.
Yanzun karfe hudu na asubah ga ladan can yana kiran assalatu.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2740598742879186&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Related posts

Leave a Comment