Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Gui?i

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Laraba, hudu ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da daya ga watan Oktoba na shekarar 2020.

  1. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan suka zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har ga shi wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  2. Majalisar Dattawa ta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar ya yi wa ‘yan Nijeriya jawabi a kan zanga-zangar da ake ci gaba da yi.
  3. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da Magashi da Olanishakin a kan zanga-zangar da ake ci gaba da yi.
  4. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya ba da umarnin girke ‘yan sandan kwantar da tarzoma a ko’ina cikin fadin kasar nan don kare rayuka da dukiyoyi daga mabarnatan da suka fake da masu zanga-zangar lumana suna aikata barna.
  5. Gwamnoni sun kafa dokar hana walwala ta sa’a ashirin da hudu a jihar Legas, da jihar Oshun, da Imo, da Edo, da Abiya, da Jos, da Ondo, da Ekiti saboda yadda ake zargin wasu zauna-gari-banza sun fake da masu zanga-zangar #ENDSARS suna aikata barna. Misali motocin da aka kona a Abuja na wajen miliyan saba’in da biyar, da gidaje da kayan ‘yan kasuwa da aka lalata har da kisa, masu kayan sun ce sai bayan da masu zanga-zangar sun gama sun wuce ne, wasu zauna-gari-banza suka biyo baya suka sa wa wuta.
  6. Gwamnatin Tarayya ta soma farautar fursunoni su wajen dubu biyu da wasu zauna-gari-banza da suka fake da masu zanga-zanga suka balle gidajen yari biyu da ke jihar Edo, suka saki fursunonin.
  7. Zuwa yanzun ‘yan sanda sun kama zauna-gari-banza su goma sha biyu da bindigogi biyar da suka diba a ofisoshin ‘yan sanda da suka kai wa farmaki a jihar Edo.
  8. Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zangar #ENDSARS su tsahirta da zanga-zangar haka nan, su bai wa gwamnati damar aiwatar da abubuwan da suka nema.
  9. Har zuwa wuraren karfe hudu na asubah ina ta leka dandalin hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC a takaice ko zan samo muku sabbin alkaluman wadanda suka harbu, ban ga sun sa ba.
  10. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilun shekarar mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi. Wasu malaman jami’a ma rabonsu da albashi wata biyar wasu shida wasu bakwai. Har da masu wata takwas.

Mu wayi gari lafiya.

Af!

A ranar Juma’a 20 ga watan Oktoba na shekarar 2017, jiya shekara uku daidai ke nan, da wuraren karfe hudu da minti 23 na asubah, na saki wannan rubutun kamar haka:

“Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, ashirin da tara ga watan muharram, shekara ta 1439 bayan hijirar cikamakin annabawa, kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin ga watan Oktoban shekarar 2017.

Saura kiris da ba a ji duriyata da asubahin nan ba saboda mu dai a kwana ukun nan, du-du-du ban yi tsammanin mun samu wutar lantarki cikakkiya ta sa’a biyu zuwa uku ba. Yanzun haka ma a duhu nake rubutu, haka muka yini haka muka kwana. Sai wata ya kare talaka ya je ya biya kudin zama a duhu, a gwamnatin da ke yaki da rashawa. Allah Ya kyauta Amin.

Jiya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Turkiyya, inda Shugaban kasar Turkiyya Erdogan ya sanar da Baba Buhari cewa, makaman nan da Hukumar Kwastam take ta kamawa, da takardunsu ke nuna daga Turkiyya ake shigo da su, takardun bogi ne, ba daga Turkiyya ake shigo da makaman ba. Daga wata kasa ake shigo da su, sai a musu takardun kasar Turkiyya. Erdogan ya ce su ma sun dukufa da binciken daga ina ake sayo makaman ake bata musu suna, ake neman hada su fada da Nijeriya.

Sai kuma a nan gida Nijeriya, da Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Sanata Misau jiya a gaban kotu, saboda tuhuma guda biyar da take masa, ta ya bata wa Babban Sifetan ‘Yan Sandan Nijeriya suna. A jiyan kotu ta ba da belin Sanata Misau, a Naira miliyan biyar da mutum biyu da zai tsaya masa. Sai dai na ga lauyoyi kusan 44 da suka yi tayin tsaya wa Sanata don kashin kan su, tunda batu ne na yaki da rashawa. Shi dai Sanata Misau ya zargi Babban Sifetan da karbar cin-hanci kafin ya yi wa ‘yan sanda karin girma ko sauyin wajen aiki, da kuma zargin yana neman ‘yan sanda mata, neman da ya saba wa aikin dan sanda.

A karshe ina kira ga malamai da limamai da ke jihar Kaduna, su taimaka yau Juma’a a dukufa ga rokon Allah, da addu’ar Allah Ya mana maganin masu satar jama’a a hanyar Abuja, suna garkuwa da su, in ba a ba su miliyan goma sha biyu ba, su kashe su.
Jama’a mu yi juma’a lafiya”

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Related posts

Leave a Comment