Saudiyya Ta Bude Kofar Umrah

Rahotanni daga Kasar Saudiyya na bayyana cewar kasar ta fitar da sanarwar cewa, ta amince da a ci gaba da ayyukan Umrah na kasa da kasa daga ranar 1 ga watan Muharram.

Sanarwar da muka samo a shafin Facebook na Haramain Sharifain, ta bayyana tsarukan da gwamnatin kasar ta fitar ga kasashen da za su zo ayyukan na Umrah.

Sanarwar ta ce, dukkan kasashen duniya za su iya turo jiragensu kai tsaye, yayin da kasar ta ware wasu kasashe tara (9) da basu amince su shigo kai tsaye ba tare da kebewar Korona ba na kwanaki 14.

Sanarwar Saudiyya | Hoto: Haramain Sharifain Source: UGC Kasashe 9 da Saudiyya ta ware cewa dole su yi kulle na Korona sun ha?a da India Pakistan Indonesia Egypt Turkey Argentina Brazil South Africa Lebanon.

Hakazalika ana bukatar dukkan mai zuwa Umrah da ya tabbatar cewa, yayi allurar rigakafin Korona AstraZeneca, Pfizer, Mordena. Sannan dole ya zama mai ziyarar Umrah ya zama daga shekaru 18 ya yi samu.

Related posts

Leave a Comment