Tsohon Mataimakin Shugaban ?asa kuma ?an takarar Shugabancin ?asa ?ar?ashin jam’iyyar adawa ta PDP Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna tsananin damuwa da takaici dangane da yawaitar sace sacen ?alibai da ake samu a makarantun Gwamnati a yankin Arewa.
Jagoran adawa ya sake jaddada kira a saka dokar ta?aci a harkar ilimi biyo bayan sace ?aliban firamare a Jihar Kaduna.
Da hantsin ranar Litinin ne wasu ‘yan bindiga suka kutsa makarantar firamare ta Rema da ke ?aramar Hukumar Birnin Gwari, inda suka yi awon gaba da ?alibai da malamai, wa?anda ba a san adadinsu ba.
Atiku ya ce ya kamata gwamnati ta tura jami’an tsaro kowace makaranta a yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan fashin daji da ke yin garkuwa da mutane don neman ku?in fansa. .
“Yayin da aka sake samun wani hari kan makaranta a Kaduna, ina sake jaddada kira ga gwamnatin tarayya ta saka dokar ta-?aci kan ilimi sannan a tura jami’an tsaro su yi gadin dukkan makarantu a yankunan da abin ya shafa,” in jis hi.
“Wajibi ne kuma mu daina biyan ku?in fansa haka kawai. Wani sau?i ne (biyan ku?in fansa) na ?an lokaci wanda zai haifar da babbar matsala a nan gaba.
“A matsayinmu na ?asa, dole ne mu tabbatar da doka da oda ko kuma mu bar wa jikokinmu gadon matsaloli. Allah ya kiyaye hakan.”
