Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a fitar wa hukumar kidaya ta kasa watau NPC, kudi domin aikin EAD a wasu bangarorin Najeriya.
The Nation ta ce shugaba Buhari ya bada umarnin a warewa hukumar NPC naira biliyan 10 domin kidaya a kananan hukumomi 546.
Ana yin wannan aiki na EAD ne domin a tsara yadda za a ji dadin kidaya mutanen da ke Nijeriya.
Haka zalika shugaban kasar ya bada umarni a ware Naira biliyan 4.5 a kasafin kudin shekara mai zuwa domin ayi aikin kidayar mutanen da ke kasar nan.
