Sace ?alibai A Katsina: Majalisa Ta Nemi Ganin Minista Da Shugabannin Tsaro Cikin Gaggawa

Majalisar dattawa ta gayyaci ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya da shugabannin tsaro da na sauran hukumomin tsaro da cewar cikin gaggawa su bayyana gaban majalisar domin ?arin haske akan matakan da suke ?auka na ceto ?aruruwan ?alibai da ‘yan Bindiga suka sace a ?arshen mako a ?aramar Hukumar ?an?ara ta Jihar Katsina.

Hakan ya biyo bayan gabatar da wani kudiri da Sanata Bello Mandiya (APC, Katsina ta Kudu) yayi, inda ya bu?aci Majalisar ta ?auki matakan gayyatar Ministan da sauran shugabannin tsaron domin yin bayani.

Sanata Mandiya ya ce satar yaran na zuwa ne a daidai lokacin da ake kan tattauna lamarin satar ‘yan matan makarantar Chibok, na jihar Borno su 270 a 2014 da kuma na Dapchi a jihar Yobe su 100 a 2018.

Ya nuna damuwa cewa idan har ba a gaggauta ceto yaran Kankara ba, makomarsu na iya shafewa a hannun yan ta’addan kamar yadda ya faru da daliban Chibok da Dapchi.

A gudunmuwa daban daban da sanatocin suka bayar, sun nuna damuwa sosai a kan ci gaban kashe kashe da sace-sacen da ke afkuwa a fadin kasar da kuma gazawar shugabannin tsaron wajen magance matsalolin.

Majalisar ta kuma bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya duba lamarin sannan ya aiwatar da shawarwarin da kwamitin majalisar kan matsalolin tsaro suka bayar.

Har ila yau ta kuma bukaci Buhari ya aiwatar da hukuncin da majalisar ta yanke a matsayin hanyoyin magance matsaloin tsaro a fadin kasar. Shugaban majalisar dattawan, Ahmad Lawan ya bukaci yan majalisar a kan kada su gaji da tattauna lamuran tsaro.

“Babu abunda yafi kare rayukan mutane muhimmanci a gwamnati. Toh wannan ne ma ainihin dalilin kafa gwamnati. “A matsayinmu na ‘yan majalisa, kada mu taba gajiya da tattauna abunda ke faruwa da mutanenmu.

Related posts

Leave a Comment