Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ?asa NCDC ta bayyana cewa mutum 49 ne ke dauke da kwayoyin cutar korona samfurin Omicron a Najeriya zuwa yanzu.
Manajan kula da shashen ya?uwar cututtuka na Hukumar NCDC, Luka Lawal, ne ya sanar haka a taron da ya yi da manema labarai a Abuja.
Lawal ya ce daga ranar Litini Najeriya ta zama ?asa ta uku a jerin kasashen Afrika da samfurin Omicron ta fi yawa baya ga kasashen Afrika ta Kudu dake da mutum 1,296 da Botswana dake da mutum 291.
Idan ba a manta ba a ranar 1 ga Disambar 2021 Najeriya ta shiga jerin kasashen duniya da samfurin Omicron ta bayyana.
Cutar ta fara bullowa a kasar Afrika ta Kudu inda bayan haka kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta sanar cewa cutar ya zama abin damuwa.
A Najeriya hukumar NCDC ta fara gano cutar a jikin wasu matafiya baki da suka shigo Najeriya daga Afrika ta Kudu.
Daga baya hukumar ta ce cutar ta ci gaba da yaduwa a kasar nan.
Zuwa yanzu samfurin Delta ce ta fi yaduwa a Najeriya inda a ranar 20 ga Disambar 2021 mutum 2,237 suke ?auke da ita.
Bisa ga alkaluman da hukumar NCDC ta fitar sun nuna cewa mutum 233,353 sannan mutum 2,991 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.
A ranar Laraba adadin yawan mutanen dake dauke da cutar ya karu daga 12,547 zuwa 16,569.
Zuwa yanzu gwamnati ta yi wa mutum 3,751,696 gwajin cutar a Najeriya.
