Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewa rundunar sojin sama ta kashe akalla ‘yan bindiga 22 a ?ananan hukumomin Jibiya da Batsari dake jihar.
Jaridar PRNigeria ta ruwaito ce wa ‘yan bindigar – wa?anda galibinsu yaran ri?a??en ?an bindigar nan ne da aka kashe Abdulkareem Boss – an kashe su ne ranar Litinin, a wani hari ta sama da dakarun rundunar ‘Hadarin Daji’ mai yaki da ‘yan bindiga – a yankin arewa maso yammacin ?asar – ta kai.
Wata majiya mai ?arfi a rundunar sojin ta shaida wa PRNigeria cewa an kai harin ne a kan tsaunukan da ‘yan bindigar ke ?oye, bayan samun bayan sirri da ke nuna cewa suna kitsa wani hari domin yin garkuwa da matafiya a kan hanyar Jibiya zuwa Katsina.
Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun addabi al’umomin yankin, inda suke yin garkuwa da mazaunan wasu yankuna a ?aramar hukumar Kankara.
Harin wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindiga da dama , ya kuma lalata sansanonin ‘yan bindigar.
A cikin watan Agustan 2022 ne dai rundunar sojin sama ta Najeriya ta kashe fitaccen ?an bindigar nan mai suna Abdulkareem Boss tare da wasu daga cikin yaransa a wani hari ta sama da rundunar ta ?addamar kan ma?oyarsu a dajin Ruga da ke jihar Katsina.
An zargi Abdulkareem da kitsi wani mummunan hari da ya yi sanadin kashe wani babban baturen ‘yan sanda a ?aramar hukumar Dutsinma ranar 5 ga watan Yulin 2022.
Mai maganar da yawun rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, wanda ya tabbatar da harin na ranar Litinin, ya ce babban hafsan sojin sama na ?asar, Air Vice Marshal Hasan Abubakar, ya umarci dakarun sojin saman ?asar da su ha?a kai da sauran jami’an tsaro domin kakkafe duka ‘yan ta’addan da kuma ma?oyarsu.
