Rikicin Kyari: Hukunci Na Karshe Na Hannun Buhari – Ministan ‘Yan Sanda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan harkokin yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buharim zai yanke hukuncin karshe kan jami’in dan sanda, Abba Kyari da ake ta tirka-tirka akai.

Dingyadi ya bayyana hakan ne a hirar da yayi a shiri ‘Politics Today’ na tashar ChannelsTV ranar Talata. Ya bayyana cewa za’a aika takardar binciken da aka yi wajen shugaba Buhari don rattafa hannu kan hukuncin da akayi masa.

An kammala bincike kan DCP Abba Kyari, IGP ya karbi rahoton Shugaban kwamitin da Sifeto Janar na yan sanda ya nada don binciken, DIG Joseph Egbunike. ya gabatar da kundin sakamakon binciken ga IGP Mohammed Alkali a ranar Alhamis, 26 ga Agusta, 2021.

IGP Alkali ya godewa kwamitin bisa aikin da sukayi kuma yayi alkawarin cewa za’a duba rahoton kuma za’a dauki matakin da ya kamata.

Ministan ya bayyana cewa yan sanda zasu bi hanyar da ta dace akan lamarin Abba Kyari. Yace, za’a nemi shawarwari na shari’a daga ofishin Babban lauya kafin a yanke hukuncin Ya kara da cewa yana da matukar muhimmanci bisa la’akari da lamarin ya shafi kasashe biyu, harma da ministan harkokin kasashen waje.

“Lamarin Abba Kyari ya bazu ko ina kuma ina tunanin mutane yanzu sunji cewa bisa jajircewa da neman adalci yan sanda sun kafa kwamitin da zasu binciki dukkanin wannan kazafin.

Mun bayyana cewa kwamitin sun mika rahoton binciken ga IGP. Mun kuma mika rahoton ga Babban lauyan kasar domin a duba a shari’ance sannan daga bisani zamu mika ga Shugaban kasa domin yanke hukuncin karshe.

Related posts

Leave a Comment