Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta lamuran addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar, da malaman addinin Musulunci da Limamai sun amince gwamnatin Buhari na iyakan kokarinta wajen yaki da annobar COVID-19 a Najeriya.
Malaman addinin, a takardar da suka ba manema labarai sun bayyana cewa lallai sun amince gwamnatin tarayya za ta gwada rigakafin Korona kafin ta ba ‘yan Najeriya.
Malaman addinin sun bayyana haka ne a taron da hukumar cigaban kiwon lafiya a Najeriya NPHDA ta shirya a Abuja domin fahimtar da su muhimmancin rigakafin Korona da kuma watsi da rade-raden cewa akwai na’urar leken asiri cikin rigakafin Koronan da za’a kawo Najeriya.
Amma a takardar da jagororin Musulman suka sanya wa hannu, sun bayyana cewa sun yarda shugaba Buhari ba zai hada baki da Turawa wajen kashe yan Najeriya ba.
“Idan Turawa na son cutar da Najeriya ta hanyar rigakafi ko wata hanya, da tuni zasu yi hakan ba tare da jiran wata annoba ba,” inji su.
“Musulmai sun amince da gwamnatin tarayya kuma duk da cewa kungiyar lafiyan duniya WHO bata amince da rigakafin ba, wajibi ne a gwada kafin ba ‘yan Najeriya.”
Daga cikin wadanda suka sanya hannu akwai sakatare janar na NSCIA, Farfesa Ishaq Oloyede; Barista Haroun Eze, Farfesa Mahmoud Eze, da Dr Faisal Shuaib.
