Rasuwa: Ta’aziyyar Rasuwar Malam Ahmad Azare, Malami Na A Sakandare – A’isha Ammani

Na tuna malamin literature ?ina a lokacin da nake ?aramar sakandiri, Ahmad Yunusa Azare. Uncle Ahmad yana da kirki matu?a gaya. A hankali yake magana saboda haka ?alibai suka sanya masa suna iri iri. ?aya daga cikin sunan da yafi shahara shine “Ezumezu” wani boka matsafi acikin littafin “The God’s Are Hungry” saboda yanda yake kiran sunan, ka san nace maka a hankali yake magana.

Ina son yanayin shigar sa, yana son shiga cikin manyan kaya. Ban ta?a ganin sa da wando da riga ba, wata?ila saboda bashi da jiki kuma bashi da tsawo.

Allah ya sani, mutum ne shi na ?warai, mai hali na gari. Ya taimake ni matu?a a wajen rubuce rubuce na. Har yanzu ina tuna kaina acikiin staff room tsaye a gaban teburun sa a yayin da yake duba rubutu na. Zai ja kurakurai na da jan biro sannan ya bani naje na ?ara gyara wa. Wasu lokutan nakan gaji har abun ya dunga bani haushi.

Bayan na gama ?aramin sakandiri, sai na bar sashen nan zuwa babban sakandiri. Wani abu da yake damuna har yanzu shine ban ta?a zuwa na gaishe shi ba, irin naje sashen ?aramin sakandiri mu gaisa. Amma lokaci zuwa lokaci nakan gan shi ya wuce ta wajen islamiyyar mu, ni kuma dana ganshi sai na gudu na ?uya.

Bayan wasu lokuta, sai na lura Uncle Ahmad bai wuce wa ta wajen islamiyyar mu. Nayi tunanin mai ya faru amma ban damu na bincika ba.

A babbar sakandiri, nafi kowa iya adabin turanci Mrs. Olabisi, malamar adabin turanci na ako da yaushe tana yabo na. A duk lokacin da ta yabe ni, sai na godewa Uncle Ahmad tare da yi masa addu’a saboda ya taimaka ?warai wajen sanya mani son darasin a zuciya ta.

A kwana a tashi, sai gani a SS2. Ranan an tashi break, ni da wasu ?an ajinmu muna hira. Muna tuna malaman mu da suka koyar damu a ?aramar sakandiri, duk wanda muka tuna sai munyi tsokaci akan sa. Sai na lura babu wanda ya ambaci sunan Uncle Ahmad don haka na tambaya;
“Uncle Ahmad fa?”
Duk suka yi shiru suna tunanin wanene Uncle Ahmad.
“Uncle Ahmad? Wanene Uncle Ahmad?” Duk suka tambaya.
“Ezumezu?” ?aya daga cikin mu ta kuma tambaya.
Na gya?a Kai alaman “Eh”. Sai duk suka fara salati, nan take jiki na yayi sanyi.
“Menene ya faru?” Na tambaya.
“Ai ya rasu, wasu watanni da suka wuce” Cewar ?aya daga cikin mu.
Ni da wasu daga cikin mu da basu da labarin mutuwarsa muka yi jim kamar ruwa ya ci mu ba tare da sanin abun da zamu ce ba.
“Ciwo yayi? Yaushe?” Na tambaya.
“Ban sani ba, amma naji an ce ya yanke jiki ne ya fa?i a wani pharmacy, ko kafin a kaishi asibiti, ya rasu kuma ance mahaifiyar sa bata da?e da rasuwa ba” ?aya daga cikin mu ta amsa.
Nayi shiru na tsawon wani lokaci, hawaye suka cika mani idanu. Nayi sororo cike da tsoro. Allah yayi masa rahama ya kyautata makwancin sa, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani amin.

Related posts

Leave a Comment