Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan lantarkin Inijiniya Abubakar D. Aliyu ya kira taron gaggawa na masu ruwa-da-tsaki domin samo mafita dangane da matsalar wutar lantarki da ta tsawwala a ‘yan kwanakin nan.
Taron ya kunshi kamfanonin samar da wutar lantarki da kuma hukumomi na gwamnati da masu zaman kansu.
A taron, wanda aka gudanar a Abuja, Injiya Abubakar D. Aliyu ya ce gwamnati ba za ta amince ba da yadda lamarin lantarki ya samu koma-baya, yana mai cewa dole a samo mafita ga dukkan matsalolin da suke kawo koma-baya ga hasken lantarki.
Ministan ya kuma gargadi hukumomi da kamfanonin su guji nunawa juna yatsa, su mayar da hankali wajen tallafawa juna wajen tabbatar da cewa ‘yan Najeriya suna samun lantarki.
Taron ya mayar da hankali ne ga duba matsalolin da suke kawo koma-baya ga harkar wutar lantarki.
Ministan ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kokarin daukar matakai domin ganin cewa an samu karuwar lantarkin da ake samarwa a Najeriya.
