Rashin Lantarki Da Tsadar Mai Na Gurgunta Gidajen Yada Labarai – BON

Hukumar kula da gidajen ya?a labarai ta ?asa BON ta bayyana karancin wutar lantarki da tsadar man dizel a matsayin wani tarna?i dake kassara ayyukan gidajen ya?a labarai a Najeriya.

A gefe guda kuma Hukumar ta koka akan yadda taurin bashi da kin biyan bashin gaba ?aya daga masu kawo tallace- tallace a matsayin wata babbar barazana ga rayuwar kafafen ya?a labarai a fa?in ?asar.

Da yake Jawabi akan gudummawar da sashin ya bayar a cigaban ?asa a shekarar da ta gabata ta 2022, babban sakataren Hukumar Dr Yemisi Bamgbose yace gwamnatin tarayya da Jihohi da sauran masu kafafen ya?a labarai su sanya himma wajen tabbatar da samun kudaden shiga da za su tallafi gidajen ya?a labarai mallakin su domin cigaban dimukura?iyya.

“Gwamnatin ta samar da ku?a?en da suka dace ga hukumar NBC domin ba ta damar samar da shirye-shirye wa?anda za su taimakawa masu ruwa da tsaki da sauran jama’a gaba ?aya.

“Shekarar da ta gabata shekara ce da hukumar samar da wutar lantarki ta samu gazawa da manyan ?alubale wajen samar da wutar lantarki amma hakan bai hana mika dogayen bill ba da sunan tana bin bashi ga kafafen ya?a labarai.

“Bamgbose wanda ya bu?aci a mayar da hankali sosai wajen inganta ayyukan gidajen rediyo da talabijin masu zaman kansu ta hanyar yin ha?aka dasu wanda zai basu damar amfani daga ku?a?en tallace-tallace.

Babban Sakataren ya kuma bada tabbacin cewa masu gidajen ya?a labarai za su cigaba da gudanar da ayyukan su bisa gaskiya kamar yadda kundin tsarin mulki ya basu ba tare da tsoro ko fargaba ba, duk da kalubalen da suke fuskanta musanman na rashin wutar lantarki.

Related posts

Leave a Comment