Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta ce rashin tausayi ne da rashin imani gwamnatin tarayya ?ar?ashin jagorancin Buhari ta yi karin farashin wutan lantarki yayinda kasar ke cikin matsin tattalin arziki, jama’a kowa yana nafsi-nafsi.
Jam’iyyar ta bayyana hakan a jawabin da ta fitar mai taken, ‘PDP ta yi watsi da guzurin sabuwar shekara na karin farashin wutan lantarki,’ ranar Talata.
A jawabin, PDP ta ce wannan karin farashin zai tsananta halin da ‘yan Najeriya ke ciki, kuma ta yi kira ga shugaba Muhammasu Buhari yayi gaggawa janye wannan kari.
Wani sashen jawabin yace, “Karin ninki biyu daga N2 zuwa N4 kan kW/hr, kamar yadda hukumar lura da wutan lantarki kasa ta sanar rashin tausayi ne, rashin hankali ne kuma zai tsananta halin talaucin da ‘yan Najeriya ke ciki a wannan lokaci.”
“Jam’iyyar ta ce dalilin da NERC ta bayar na wannan kari basu gamsar ba, musamman yanzu da ‘yan Najeriya ke zaton gwamnati zata fito da tsare-tsaren rage illar matsin tattalin arziki.”
An ruwaito cewa hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC, ta karyata rahoton cewa ta kara farashin wutan lantarki na kashi 50 kan abinda jama’a ke biya yanzu a fadin tarayya. NERC a shafinta na Tuwita ta bayyana cewa har yanzu bata bada umurnin kara farashin wuta ba kamar yadda kafafen yada labarai ke watsawa amma unguwannin masu kudi kawai aka karawa.
