Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar an ?aura auren ?an shugaban ?asa da ?ar gidan sarautar Kano ba tare da ganin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ba a wajen ?aurin auren.
An ?aura auren Yusuf Buhari da ?ar Sarkin Bichi Zahra Nasiru Ado Bayero a garin Bichi.
Kuma baya ga Sarkin Kano, manyan sarakunan jihar Kano ba su halarci ?aurin auren ba, ko da yake Sarkin Gaya ya tura wakilinsa.
Sarkin Kano Aminu Ado da Sarkin Bichi Nasiru Ado dukkaninsu ?a?an marigayi Sarki Ado Bayero ne.Kuma Sarkin Kano Aminu Ado shi ne babba.
Wasu na ganin Sarkin Kano Aminu Ado ya ?auracewa ?aurin auren ne saboda ba a kai ?aurin auren a Masarautarsa ba, yayin da kuma wasu ke cewa Sarkin ya tsaya ne tarbon ba?i.
Batun ya ja hankali, kasancewar manyan Sarakunan na Kano ?an gida ?aya ne. Kuma ?aurin auren gidan Ado Bayero.
Sai dai wasu masana harkokin fadar Kano sun ce a al’adance Sarki ba ya halartar daurin aure a wani waje sai dai a fadarsa.
A masarautar Kano aka ?aura auren ?ar gidan Dangote da kuma ?ar Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.
