Ranar Ma’aikata: Nauyi Ne A Kanmu Mu Inganta Rayuwar Ma’aikata – Shugaban Kasa

IMG 20240308 WA0066

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban ?asa Bola Tinubu ya ce akwai bu?atar ganin an kyautata wa ma’aikata a Najeriya ta hanyar biyan su albashin da ya dace da kuma inganta walwalarsu.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin sa?on da ya fitar na taya murnar ranar ma’aikata ta duniya, wanda ake gudanarwa a ranar ?aya ga watan Mayu na kowace shekara.

Bukin ranar ma’aikatan na zuwa ne a lokacin da ma’aikatan Najeriya ke kokawa kan tsananin rayuwa sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi da kuma zubewar darajar ku?in ?asar.

A cikin sa?on shugaba Tinubu, wanda ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkar ya?a labaru, Ajuri Ngelale, ya ce ba wai kawai albashin ma’aikata ya kamata a inganta ba, har ma da kayan aiki.

Related posts

Leave a Comment