Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar a?alla mutum 9 ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai rugar Fulani a ?aramar hukumar Mashegu ta jihar Neja.
Harin wanda ake zargin yan Bijilanti daga ?auyen Maza Kuka ne suka aiwatar, ya faru tsakanin ranar Lahadi zuwa Litinin. Hakazalika ana tsammanin na ?aukar fansa ne kan abinda ya faru ranar 25 ga watan Oktoba a masallacin garin Maza-Kuka.
?aya daga cikin wa?anda lamarin ya shafa, Shehu Mohammadu, yace: “Yan bijilanti sun shigo ?auyen mu, suka ?ona gidajen mu, sannan suka gudu. Matar ?anina da ?an jaririnta sun rasa ransu.” “Sun kuma kashe wani ?ani na, da ?ansa ?an shekara 3, sun dai kashe mun ‘yan uwana 7, kuma dole na gudu in ba haka ba nima da sun kashe ni.”
“Mun bar ?auyen, yanzun ina rayuwa a wani wuri mai nisa, kuma ba zan koma ?auyen ba, domin nima kashe ni za su yi.” Shaidan da lamarin ya faru a idonsa, Alhaji Muhammadu Marike, yace yanzun haka yana gudun hijira ne a wajen jihar Neja.
“Banda harin da suka kashe dagacin garin Adogon Malam da ?an uwansa, sun sake dawo wa. Sa’ar dana ci shine ?aya daga cikinsu ya sanni, shine yace a kyale ni.” “Sun tafi da mutum 8, har yanzun babu wanda yasan inda suke.
Kakakin yan sanda reshen jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, yace hukumarsu ta tura da ?arin jami’an yan sanda domin kame masu hannu a harin. Ya kuma yi kira ga al’umma su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri domin tabbatar da doka ta yi aikinta akan wa?an da suka aikata wannan ?anyen aiki.
