Peter Obi Bai Shirya Kalubalantar Nasarar Tìnubu Ba – Kotun Zabe

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta caccaki jam’iyyar Labour da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, kan rashin shiryawa karar da aka shigar na kalubalantar nasarar Shugaba Bola Tinubu.

A ci gaban zaman kotun a ranar Alhamis, daya daga cikin manyan lauyoyin da ke cikin tawagar lauyoyin masu shigar da kara, Emeka Okpoko, ya nemi gabatar da takardun zabe a matsayin shaida a gaban kotu amma an ce ba a gabatar da takardun yadda ya kamata ba kuma ba a shirya su a gaban kotun ba.

Don haka kotun ta dage sauraron karar na tsawon mintuna 10 sannan ta bukaci tawagar lauyoyin da ta sake gabatar da jadawalin takardun kamar yadda aka tanadar da rahoton gabanin sauraron karar.

Duk da haka, bayan da kotun ta dawo, tawagar lauyoyin ta kasance cikin rashin tsari.

Cikin rashin jin dadi, kwamitin mutum biyar na alkalan kotun karkashin jagorancin Haruna Tsammani, ya shawarci masu shigar da karar da su nemi a dage zamansu domin su tsara takardunsu yadda ya kamata.

Sun bayyana abin da aka yi a yau a matsayin bata lokaci, inda suka ce lauyoyin masu shigar da karar sun raina muhimmancin aikin da ya kamata su yi.

Da yake mayar da martani, Awa Kalu, wani babban lauya a tawagar masu shigar da karar, ya ce ba za su karbi shawarar dage zaman ba, sai dai za su mika shaidun kananan hukumomi 16 da ke kasa.

Related posts

Leave a Comment