Pantami Zai Jagoranci Zaman Tattaunawa Da Tiwita

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Minista Pantami, da Babatunde Fashola, ministan ayyuka da gidaje, Abubakar Malami, Antoni janar na tarayya da su tattauna da Twitter kan dakatar da ita da aka yi a Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta haramta Twitter a Najeriya tun bayan zargin kafar sada zumuntar da aka yi da katsalandan, a harkokin cikin gidan Najeriya ta hanyar goge rubutun Shugaban kasa.

Duk da matsantawa da aka yi daga kasashen ketare da kungiyoyi, gwamnatin Buhari ta cigaba da tsayuwa kan matsayarta na ladabtar da kamfanin na Tiwita.

Amma a wata takarda da aka fitar a ranar Talata, Lai Mohammed, minsitan yada labarai, ya sanar da cewa gwamnatin tarayya ta kafa kungiyar wadanda zasu tattauna da Twitter, domin kawo karshen matsalar.

Baya da Pantami Fashola da Malami, sauran ministocin da zasu tatttauna da Twitter sun hada da ministan Chris Ngige, ministan kwadago da kuma Geoffrey Onyeama, ministan harkokin waje.

Related posts

Leave a Comment