Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bawa hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) da hukumar kula da shaidan dan kasa (NIMC) umurnin dakatar da chajin naira 20 da ake cirewa masu neman sanin nombobin NIN dinsu a layukansu.
Umarnin Ministan wanda ya fara aiki nan take, da nufin sau?a?ewa al’ummar Nijeriya aikin cikin araha.
Ga duk mai bukatan sanin nomban katin shaidar zama dan kasa (NIN) ya danna *346# a layinshi, ba tare da sun chaje shi ko Naira ba daga yanzu har lokacin da zaa kulle yin ragistar layuka da katin dan kasa.
Minista Pantami dai na cigaba da shan suka ga’yan Najeriya tun bayan da ya ayyana cewar za’a rufe layukan wayoyin dukkanin wa?anda basu yi rijistar layukan wayoyin su da lambar katin shaidar zama ?an kasa ba.
