Obasanjo Da Atiku Duk Mayaudara Ne – Tinubu

?an takarar shugabancin Najeriya a ?ar?ashin jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya shawarci al’ummar jihohin Kudu maso Gabas cewa kada su bi ra’ayin Obasanjo kuma kada su za?i Atiku a za?en shugaban ?asa, domin mayaudara ne.

A ranar Laraba ce Tinubu ya bayyana haka a wurin kamfen a Enugu.

Tinubu ya garga?e su cewa su tuna irin yaudarar da Obasanjo da Atiku su ka yi masu a lokacin da su ke kan mulki.

Ya ce PDP a lokacin su ta yi al?awurra da dama ga yankin, amma ba ta cika ba.

Ya buga misali da gadar Kogin Neja da ke Lokaja ta biyu, wadda mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala kwanan nan.

Tinubu ya ce shi ma Atiku yaudarar yankin Kudu maso Gabas zai yi da ya ke cewa idan ya zama shugaban ?asa ?an ?abilar Igbo ne zai gaje shi.

Asiwaju dai ya ragargaji Obasanjo ne saboda ya fito a fili cikin wata wasi?ar da ya fitar ya bayyana ra’ayin cewa Peter Obi na LP ne ya fi cancanta a za?a, ba Atiku ko Tinubu ba.

“Kada ku ri?a ?ata lokacin saurare da amincewa ga al?awurran Obasanjo da Atiku. Su biyun duk mayaudara ne. Sun da?e su na yaudarar ku tun daga 1999 har yau ba su daina ba,” cewar Tinubu.

Tinubu ya yi i?irarin cewa Obasanjo da sauran shugabannin da su ka wuce na PDP sun kasa cika al?awarin gina Gadar Kogin Neja, wadda ta ha?e Arewa da Kudu, amma sai yanzu mulkin APC ya kammala gadar.

Related posts

Leave a Comment