Rahotannin dake shigo mana daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar an tsinci gawar wasu yara biyu a baraguzan wani bandaki na makarantar Firamare ta tunawa da UK Bello, a Paiko, karamar hukumar Paikaro ta Jihar Neja.
Har ya zuwa lokacin rubuta rahoton ba a tabbatar da abin da yaran ke yi ba a wurin yayi da ginin da aka ce ya tsufa dama ya rufta musu.
An samu mabanbantan rahotanni akan yaran da suka rasun, wasu na fa?in cewar yaran ‘yan makaranta ne a makarantar.
Wasu majiyoyi sun ce yaran, namiji da mace, suna tallar Pure water ne tare da abokansu a kusa da makarantar a lokacin da ginin ya rufta musu, suka mutu nan take.
Wasu kuma sun ce yaran suna roron kayayyakin karafuna ne da za su sayar a kusa da ginin a lokacin da ya rufta.
Dukkanin kokarin da aka yi na jin ta bakin Hukumar makarantar abin ya ci tura.
