Labarin dake shigo mana yanzu daga Minna fadar gwamnatin jihar Neja na bayyana cewar Gwamnan Jihar ya ce ‘yan bindiga sun kashe mutum a?alla 220 a jiharsa cikin wannan watan na Janairu ka?ai a hare-haren da suka kai yankuna 300.
Da yake magana da manema labarai jim ka?an bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja ranar Talata, Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce cikin wa?anda aka kashe akwai jami’an tsaro 25 da kuma ‘yan sa-kai 30.
Ya ?ara da cewa ‘yan bindigar da ake yi wa la?abi da ‘yan fashin daji sun sace mutum 200 a watan na Janairu
