NDLEA Ta Damke Mutumin Dake Harkar Muggan Kwayoyi Da Kyari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar NDLEA mai ya?i da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta cafke Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, ?asurgumin dillalin ?wayoyi, wanda shi ne ummul-aba-isi na cinikin ?wayar Tramadol ta Naira Biliyan 3, wacce a ke tuhumar dakataccen ?an sandan nan, Abba Kyari.

Ukatu, wanda shine Shugaban Rukunin Kamfanin Mallison, dubun sa ta cika ne bayan watanni a na fakon sa kuma ana ta kulli-kurciya da shi.

An dai cafke shi ne a cikin jirgin sama a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas a kan hanyarsa ta zuwa Abuja a ranar Laraba, 13 ga watan Afrilu.

Binciken hukumar NDLEA ya bayyana cewa shi ne babban dillalin shigo da ?wayar Tramadol mai nau’i daban-daban da su ka ha?a da mai ?arfin giram 120, 200, 225 da 250 cikin ?asar nan.

Ukatu na da kamfanin magunguna da na robobi, in da ya ke amfani da su wajen yin basaja domin ya shigo da miyagun ?wayoyi cikin ?asar nan, inda kuma a ka gano ya na da asusun banki har 103 da ya ke amfani da su wajen bada?alar ku?a?e.

An fara sanya ido a kan Ukatu ne a Bara bayan da a ka kama wani ma’aikacin sa da katan 5 na Tramadol mai nauyin giram 225 a ranar 24 ga watan Mayu, 2021 lokacin da ya tafi ya sayar wa da wani ?an sanda da ya ke cikin tawogar Abba Kyari kuma yayi basaja a matsayin mai sayen ?wayoyi a Ikeja ta Jihar Legas.

A tuna cewa Kyari tare da wasu mutane hu?u na tawogar sa na fuskantar Shari’a a Babbar Kotun Taraiya a Abuja a kan irin wannan laifin.

Related posts

Leave a Comment