Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Kwamishinan raya karkara na Jihar Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce za su ?aukaka kara a kan hukuncin nasarar bangaren Shekarau akan Shugabancin jam’iyya wanda babbar kotun da ke Abuja ta yanke, kuma ta ?ara jaddada shi.
A cewarsa ”Akwai kotu ta gaba ta daukaka kara, kuma za mu daukaka, muna sa ran za a yi mana adalci a warware wannan hukunci, don a baya ma ba a duba hujjujojin da muka kawo ba aka yanke hukunci,
”Babu maganar Danzago kwata kwata a shugabancin APC a Kano, domin ai ba da ka ake shugabancin jam’iyya ba, ba al’amari ne na wasa ba, su da suke da’awar shugabanci ai ba su yi za?en ba, kuma babu wanda ya turo musu jami’ai daga shalkwatar jam’iyya ta kasa” inji shi.
Rikicin da ke tsakanin ?angaren Ganduje da na Shekarau a Kano ya yi sanadin rabuwar jam’iyyar gida biyu inda Ahmadu Haruna Zago ke jagorantar ?angaren Shekarau sai kuma Abdullahi Abbas ?angaren Ganduje.
Wasu na ganin rabuwar kan APC a Kano wata babbar ?araka ce ga jam’iyyar a Najeriya musamman yanzu da ake tunkarar za?en 2023
