Najeriya Za Ta Murmure Nan Da Shekara Guda – Shettima

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Mataimakin shugaban ?asa Kashim Shettima, ya ce Najeriya za ta samu kyakkyawan sauyi nan da wata tara zuwa shekara ?aya karkashin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Mataimakin shugaban ?asar ya bayar da tabbacin ne a ranar Juma’a a birnin St Petersburg yayin wani zama da al’ummar ?an Najeriya mazauna Rasha.

Kashim ya tabbatarwa ?an Najeriya musamman ma wa?anda ke zaune a ?asar Rasha, cewa gwamnatin Tinubu za ta yi aiki tukuru don kawo ci gaba.A lokacin da yake tattaunawa da ?an Najeriya a Rasha, Kashim ya ce “ina tabbatar muku cewa nan da wata tara zuwa shekara ?aya, za a samu sauyi mai kyau a Najeriya, na fa?i haka ne saboda na yi imani da irin hazakar da Shugaba Bola Tinubu ke da shi.”

Ya ce gwamnati mai ci na yin duk ?o?arinta wajen kyautata yanayin tattalin arzikin ?asar da kuma farfa?o da kamfanoni da za su kawo mata ci gaba.

Related posts

Leave a Comment