Najeriya Za Ta Kai Ga Nasara Muddin An Bi Tafarkin Magabata – Paul Unongo

An bayyana cewar hanya guda da ta rage wa Najeriya na kai wa ga gaci shine bin tafarkin magabatan kasar na farko sau da ?afa, wato Sardaunan Sokoto, Awolowo da Ezikwe.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin ?aya daga cikin Dattawan Arewa kuma tsohon Ministan hasken Lantarki a Jamhuriya ta biyu Dr Paul Unongo a yayin wata tattaunawa da gidan Talabijin da Rediyo na Liberty Abuja ya yi dashi, akan halin da Najeriya ta tsinci kanta ciki da kuma samun mafita.

Dattijon ya ?ara da cewar, a zamanin da Najeriya ta samu ‘yancin kai a jamhuriya ta farko, shugabannin yankuna uku na ?asar Shiyyar Arewa da Yamma da Shiyyar Gabas, abin da suka sanya a gaba shine kishin ?asar, wannan ya sanya a wancan lokacin Najeriya ta yi nasarar zama Giwar Afirka Jagorar Kasashen Nahiyar.

“Abin da ya biyo baya a yanzu shine ‘yan Najeriya sun rasa wancan matsayi da suke da shi sakamakon son zuciya da nuna ?angaranci da rashin kishi, lamarin da ya jefa Jama’ar ?asar cikin mawuyacin hali.

Dr Unongo wanda ya koka sosai da halin da yankin Arewa ya shiga ciki a halin yanzu na ta?ar?arewar tsaro, da kashe-kashe gami da rashin kwanciyar hankali a kullum, inda ya ?ora alhakin hakan akan sakin layi da aka yi daga ainihin turbar kwarai da marigayi Sardauna ya ?ora yankin a kai.

Dangane da barazanar da wasu jama’a ke yi musanman yankin Kudancin ?asar na cewar za su ?alle ko a sake fasalta kundin tsarin mulki ko a kira babban taro na ?asa, Dattijon Paul Unongo ya tunatar da su komawa baya cikin tarihi lokacin da aka yi ha?akar 1914, wannan tsarin irin shine kasashen duniya da suka cigaba Turai da Amurka ke amfani da shi na zaman tare, muddin muka fahimci muhimmancin zaman tare muka sanya kishin kasa, babu shakka Najeriya zata zama cikin manyan kasashen duniya da ake tinkaho da su.

Related posts

Leave a Comment