Nadin Sabbin Hafsoshin Tsaro: Manyan Hafsoshi 100 Za Su Yi Ritayar Dole

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar akwai yiwuwar manyan hafsoshin soji masu mukamin janar-janar, birgediya-Janar, air vice marshal da admiral a rundunonin sojin sama, kasa da ta ruwa za su yi murabus ala tilas biyo bayan nadin sabbin hafsoshin tsaro da shugaba Tinbu ya yi.

Sakamakon wannan murabus, wanda ya zama tilas, akwai wasu hafsoshin soji da za su samu karin girma don maye gurbin wadanda suka ajiye aiki, a wani bangare na sake fasalin rundunonin da sabbin hafsoshin tsaron za su yi.

Related posts

Leave a Comment