Fitaccen Farfesan Najeriya, kuma shahararren marubucin Duniya, Wole Soyinka, ya yi tir da salon da aka bi wajen kama shugaban ?ungiyar tsagerun Inyamurai ta IPOB Nnamdi Kanu.
Babban marubucin ya zargi gwamnatin tarayya da shugaba Muhammadu Buhari yake jagoranta da yin garkuwa da Nnamdi Kanu daga inda yake a ketare.
Farfesan ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da BBC sashin Pidgin ya yi da shi a ranar Litinin, 2021.
A cewar Wole Soyinka, hayaniya za ta kicime idan har aka yi wa ‘yan kasa cikakken bayanin gaskiyar yadda aka cafko Kanu daga kasar wajen da yake. Idan aka san gaskiya, sama da kasa za su hade “Ba aiki na ba ne in fada wa shugaban kasa ya shirya, domin ko ina zai amsa a lokacin da gaskiyar kamun Kanu ya fito fili.”
“Mutane suna ta ‘yan surutai, a ce wannan, kuma ace wancan. Ana kokwanton ko Najeriya ta bi dokokin kasashen ketare.”
“Abu na biyu shi ne abubuwan da Kanu ya rika yi a wajen kasar nan. Ya yi ta furta kalaman batanci, wanda hakan abin takaici ne daga gare sa.” Sai dai inda za a samu matsala shi ne, dokar kasa ce kurum za ta iya hukunta laifin kalaman batanci.
“Ya dace ayi garkuwa da shi? Za a iya cewa ram da shi aka yi, amma garkuwa da shi aka yi. Hakan ya saba dokar waje, ya ci karo da abin da ya kamata.” Farfesa Soyinka ya ce gwamnatin tarayya ta gaza cafke ‘yan bindigan da su ke yi wa mutane barna, amma ta iya wuf ta kama shugaban na kungiyar IPOB.
Soyinka ya ce tun farko ya kamata a ce shugaba Muhammadu Buhari ya yi maganin irinsu Miyetti Allah, ba sai daga bayan nan zai ce zai ce zai casa su ba.
