Na Lashe Shekaru Ina Sayar Da Mushen Kaji A Maiduguri – Ebere

Rundunar jami’an tsaron farin kaya Civil Defence a Jihar Borno ta yi nasarar damke wani mutum da ya da?e yana safarar mushen kaji gami da sayarwa jama’a a Jihar Borno tsawon shekaru.

Lokacin da yake amsa tambayoyi a helkwatar rundunar, ya tabbatar da cewar a kalla ya yi nasarar sayar da Mushen Kaji sama dubu bakwai a Jihar Borno da kewaye.

?an kimanin shekaru 33 Mutumin mai suna Hassan Ebere, ya ?ara da cewar bai san adadin shekarun da ya shafe yana gudanar da muguwar sana’ar ba a Maiduguri da kewaye.

“Kasancewata Maraya ne ya jefani shiga cikin wannan mummunan aiki domin samun rufin asiri, amma na yi nadama kuma da yardar Allah ba zan sake ba”.

Rundunar tsaron farin kayan ta bayyana cewar bayan ta kammala binciken ta za ta iza ?eyar Ebere kotu domin girbar abin da ya shuka.

Related posts

Leave a Comment