Na Gamu Da Manyan Kalubale A Masana’antar Kannywood – ‘Yar Agadez


Fitacciyar jaruma a Masana’antar fina-finai ta Kannywood Masauda Ibrahim wacce aka fina da Yar’agadaz ,wacce kuma ta yi suna a cikin shirin Dadin Kowa wato Zuby, ta bayyana irin wahalar da ta sha a harkar fim kafin ta samu ta zama fitacciyar jaruma.

Masa’uda’ Yar’agadaz ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawarta da wakilin Jaridar Dimokuradiyya, inda ta fara da cewar :

“To gaskiya na sha wahala, kuma na hadu da Kalubale da dama a cikin harkar fim musamman ma dai sai ka ga wani ya nuna yana son ka a fili, sai ka tafi kuma ya zage ka, to irin wannan na fuskance su da dama, sai dai ina yi musu fatan alheri, saboda yanzu komai ya wuce a waje na, domin idan na ce zan tsaya na lissafa to abubuwan suna da yawa. ”

Dangane da maganar aure kuwa da muka tambaye ta cewa ta yi:

“Ni dai a gare ni zabin Allah na ke nema, duk wanda Allah ya zaba miun shi zan aura, don haka duk masu yi mana kallon muna da buri, to mu ba haka mu ke ba, domin arziki na Allah ne, don haka ba sai lallai mai kudi zan aura ba, miji nagari kawai na ke fatan samu. ” a cewar ta.

Related posts

Leave a Comment