Ministar Harkokin Agaji da Jin?ai, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta amince a yi biya na ?arshe ga ‘yan rukuni biyu na masu cin moriyar shirin tallafi na N-Power wanda ?aya ne daga cikin shirye-shiyen gwamnati na agaza wa matasa.
Wata sanarwa da mai taimaka wa ministar kan ya?a labarai, Madam Nneka Anibeze, ta rattaba wa hannu, ta bayyana cewa ministar ta bada umarnin ne a ranar Litinin, 24 ga Agusta, 2020.
A cewar ta, ministar ta bada umarnin a biya ku?in ne ga masu cin moriyar shirin na N-Power a Rukunnan A da B.
Ta ce, “Har an mi?a takardar umarnin a yi biyan har zuwa na watan Yuni, 2020 na rukunnan biyu ga ofishin Akanta Janar na Tarayya (AGF) domin su yi tantancewar ?arshe kuma su biya.
“Biyan da kawai ya rage, wanda ke jiyan a tura takardun zuwa ofishin Akanta-Janar na Tarayya, shi ne na watan Yuli na masu cin moriyar a Rukunin B,” inji ta.
Bugu da ?ari, ministar ta yi bayanin cewa masu cin moriyar shirin wajen mutum 14,000 wa?anda ofishin Akanta-Janar ya tsallake su a lokacin biyan watan Maris zuwa Yuni, 2020 za su iya kasancewa cikin wa?anda na’urar GIPMIS da ake biya da ita ta ?i shigar da sunayen su saboda akasin bayanai da ta gani game da asusun su na banki kamar yadda ma’aikatar ta tura wa ofishin Akanta-Janar.
Ta nanata cewa rahoton da aka samu daga ofishin Akanta-Janar ya nuna cewar duk wanda ke samun biyan ku?i daga wasu hukumomin gwamnati, na’urar biya da ake kira ‘Government Integrated Financial Management System’ (GIPMIS) ba za ta amince ta biya shi wannan ku?in ba, za ta ri?e su.
Hajiya Sadiya ta bayyana cewa ta bu?aci ofishin Akanta-Janar ?in ya turo mata sunayen wa?anda abin ya shafa tare da dalilin rashin biyan nasu, kuma ta yi al?awarin za ta sanar da wa?anda abin ya shafa.
Ta ?ara da cewa idan an ?i biyan su ne a bisa kuskure, to wa?anda abin ya shafi su sani cewa za a biya su dukkan ku?in su da zaran ofishin Akanta-Janar ya gyara kuskuren da aka samu.
Har ila yau, ministar ta bayyana cewa Rukunnan A da B na masu cin gajiyar shirin na N-Power sun riga sun sani tun daga farko, tunda da dai an fa?a masu, cewa da ma wa’adin shirin na tsawon watanni 24 ne.
Ta ?ara da cewa rashin cire masu cin moriyar shirin na Rukunin A bayan sun cika watanni 24 ya faru ne saboda matsalolin da aka samu a lokacin.
Ta ce, “Saboda haka, wa?anda wa’adin su ya ?are a Rukunin A bayan watanni 40 da Rukunin B bayan watanni 24 ya yi daidai da ?a’idar da aka yi da su a lokacin da aka ?auke su.
“Wannan ya yi daidai da abin da ya faru lokacin da aka dawo da shirin na N-Power a ?ar?ashin ma’aikatar a ?arshen shekarar da ta gabata, wato babu wani tsari da aka yi masu na cewar za a ?auke su aiki kai-tsaye a gwamnati ko a kamfanoni masu zaman kan su ko a saka su cikin wata harkar sana’a kafin a maida shirin a ?ar?ashin ma’aikatar.”
Ministar ta shawarci wa?anda wa’adin su ya zo ?arshe a shirin da su ci gaba da ha?uri domin ta na wani ?o?ari ta tuntu?ar hukumomin gwamnati daban-daban, ciki har da Babban Bankin Nijeriya (CBN) da Ma’aikatar Aikin Gona da Inganta Karkara ta Tarayya don ganin yiwuwar sun shigar da wa?anda su ka ci moriyar shirin zuwa cikin wasu shirye-shirye na gwamnati ko ma a ba su aiki idan ya samu.
Ta ce: “Mun bu?aci ma’aikatan shirin da ke dukkan jihohi da su ba mu sunaye da cikakken bayani na wa?anda wa’adin su na cin moriyar shirin na N-Power ya cika wa?anda ke da ra’ayin shiga tsari na gaba na ma’aikatar mu.”
Hajiya Sadiya ta kuma bayyana cewa za a yi wa masu cin moriyar shirin a Rukunin C da za a fara da su nan gaba ka?an cikakken bayani kan shigar su shirin da iyakar wa’adin sa a daidai lokacin shigar su, don kauce wa rashin fahimtar da ta faru game da ‘yan Rukunnan A da B.
Ta ?ara da cewa za a yi cikakken shiri tun kafin wa’adin zaman su cikin shirin ya cika don kauce wa abin da ke faruwa a yanzu.
Ta ce, “Za a yi aikin tantancewa sosai na wa?anda ke son su shiga shirin a Rukunin C don tabbatar da an za?i wa?anda su ka dace.
“Ma’aikatar za ta yi aikin tantancewar a bayyane ba tare da wata ?umbiya-?umbiya ba wajen za?en wa?anda su ka cancanta daga cikin mutane 5,000,000 (milyan biyar) da su ka cike takardun neman shiga shirin.
“An tsara shirin N-Power ne domin a taimaka wa matasa ‘yan Nijeriya ‘yan shekara tsakanin 18 zuwa 35 domin su samu ?warewar da za ta taimaki rayuwar su don su zama masu kawo sauyi a cikin al’ummar su kuma su kasance masu fa?a a ji a harkar kasuwanci a gida da waje, kuma za a ri?a ba su ku?in agaji N30,000 a kowane wata.”
