?ungiyar Kafafen ya?a labarai na Shiyyar Arewacin Najeriya (NMF) sun nuna ki?imewa da juyayin rashin ?aya daga cikin jigogin ?ungiyar mawallafin Jaridun Lerdership Mista Sam Nda-Isaiah Kakakin Nupe wanda ya rasu a ?arshen makon da ya gabata.
A cikin wata takardar sanarwa da kungiyar ta fitar wadda ta samu sanya hannun Shugaban Kungiyar Dan Agbese, sun bayyana Mutuwar Sam Nda-Isaiah a matsayin wani rashi da har abada Duniyar Jaridu da rubuce-rubuce ba zasu manta ba duba da irin gudummuwar da Marigayin ya bayar ta wannan fannin.
Sam Nda-Isaiah ya kasance wani Mutum mai fikira wanda kalaman shi suka kasance abin ji da sauraro, ya yi rawar gani rayuwar shi wajen Ilimantarwa da fadakar da al’umma musanman talakawa da sauran ‘yan ?asa wanda kowa ya shaida hakan.
Sam Nda-Isaiah ya kasance gagara badau ta fuskar fadakarwa da sanar da jama’a ‘yanci da hakkin su, lamarin da ya sanya kowa a fa?in Najeriya ke Allah san barka.
Yunkurin Marigayin na fa?a?a fannin ya?a labarai zuwa ga samar da Gidajen Rediyo da Talabijin mallakar Kamfanin shi, wani abu ne da ba za a manta ba, duk da Allah bai nufe shi da yin tsawon rai har ya zuwa lokacin da mafarkin shi zai tabbata.
Ya kasance garkuwa kuma bango ga dinbim jama’a musamman Matasa ta fuskar samar musu da ayyukan yi, ya dauki jama’a da dama aiki a karkashin kamfanin shi Lerdership.
Muna addu’ar samun jin kai da rahamar Ubangiji a gareshi, tare da addu’ar Allah albarkaci bayan shi, da zuriyar da ya bari Allahumma Amin.
