Muna Da Rawar Takawa Wajen Magance Matsalolin Najeriya – Matan Gwamnoni

Kamar yadda suka saba, lokaci zuwa lokaci, kungiyar matan gwamnoni sun yi taro a Abuja, wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa a jiya Litinin, 7 ga watan June 2021.

Uwar Gidan gwamnan Ekiti Erelu Bisi Fayemi ita ce ta jagoranci tattaunawar da aka gudanar.

A lokacin zaman kungiyar matan gwamnonin sun tattauna akan matsaloli daban-daban wanda ya shafi yanayin tsaro, matsalar da ta shafi mata da yara na fyade, cin zarafi, da hanyoyin taimakawa mata wajen al’amurran rayuwar yau da kullum.

Haka zalika matan gwamnonin sun nema hanyoyin hadin guiwa da kungiyar gwamnoni domin ganin an zakulo hanyoyin taimakawa mata da yara kanana, da kuma yin dokoki da za su bada kariya ga lamarin tare da kyautata jin dadin al’ummar kasa baki daya.

Related posts

Leave a Comment