Mun Yi Damarar Samun Nasarar Yakubu Lado A Takarar Gwamnan Katsina – Imrana Nas

Shugaban kwamitin ya?a labarai na yakin neman za?en Atiku/Lado na Jihar Katsina Alhaji Imrana Nas Shugaban Talakawa ya bayyana aniyar kwamitin nasu na ganin ?an takarar Gwamnan jihar Katsina karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Yakubu Lado ?anmarke ya yi nasara a za?en dake tafe.

Imrana Nas ya bayyana hakan ne a yayin ganawar sa da manema labarai a Katsina jim ka?an bayan ?addamar da kwamitin nasu da ya gudana a sakatariyar jam’iyar PDP dake Jíhar.

Shugaban kwamitin ya?a labaran ya ?ara da cewar a fili yake jama’ar Jihar Katsina suna cikin wani mawuyacin hali na tagayyara wanda suke bu?atar ?auki cikin gaggawa kuma tabbas Yakubu Lado shine mafita kasancewar shi gogaggen ?an siyasa wanda ya fara tun daga matakin Kansila har ya zuwa Sanata.

Imrana Nas ya bayyana APC a matsayin matacciyar jam’iyya wadda ta mutu tuni shure-shure kawai take a yanzu bisa ga la’akari da yadda jama’a masu manufa suke ta ficewa daga cikinta zuwa PDP, mutane irin su tsohon sakataren gwamnatin jihar Alhaji Mustapha Inuwa da sauran manyan ?usoshin Jamiyyar.

Daga karshe Alhaji Imrana Nas ya yi kira ga jama’ar jihar Katsina da su yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin samun nasarar PDP da ?an takarar gwamnanta Alhaji Yakubu Lado a babban za?en dake tafe na shekarar 2023.

Related posts

Leave a Comment