Mun Yi Azumin Shekaru Takwas Karkashin Mulkin Janar Buhari – Kungiyar Kwadago

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar ?wadago ta kasa ta ce ma’aikatan ?asar na cikin wani hali, kuma babu wani sauyin a zo a gani da aka samu tun bayan kama mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

A wata tattaunawa da BBC, albarkacin ranar ?wadago ta duniya, sakataren ?ungiyar ?wadago ta Najeriya, Kwamared Nasir Kabir ya ce ci gaba ka?an ne kawai za a iya cewa ma’aikata sun samu a ?ar?ashin gwamnati mai ci.

Ya ce “abin farin ciki ne sake zagayowar ranar ma’aikata ta duniya, amma maganar gaskiya al’amuran da ma’aikata (a Najeriya) suke ciki da abubuwan da suke fama da su ba abin murna ko farin ciki ba ne.”

Abubuwan da ya bayyana cewa su ne manyan ?alubalen da ma’aikata a Najeriya ke fuskanta su ne:

Tashin farashin kayan masarufi
Rashin isassun ku?i a hannu
Biyan ku?in makarantar yara
Tsadar wutar lantarki
Tsadar man fetur
Ku?in kiwon lafiya.

A cewar kwamared Nasir ?arancin albashin ma’aikata a Najeriya ba zai ishi magidanci ya sayi buhun shinkafa da zai ciyar da iyalansa ba.

A cewarsa “idan ka duba a halin yanzu ma’aikaci a Najeriya na cikin hali ne na lahaula.”

A lokacin da aka tambaye shi ko ma’aikata sun samu ci gaba ?ar?ashin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, sai ya ce “ban da ci baya, babu abin da ma’aikata suka gani.”

Kwamared Nasir ya ce wuri ?aya tilo kawai da ma’aikata suka samu ci gaba a lokacin mulkin shugaba Buhari shi ne batun biyan albashi.

Ya ce “abu ?aya wanda muka gani wanda shi ne za mu iya cewa za mu yaba wa wannan gwamnati shi ne maganar biyan albashi.”

“Da gaske sun biya albashi kuma suna biya babu tsaiko, amma maganar gaskiya ita ce albashin bai taka kara ya karya ba tunda ba ya isan ma’aikata,” in ji shi.

Related posts

Leave a Comment