Mun Kwato Fiye Da Dala Biliyan Guda Daga Barayin Gwamnati – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ?ar?ashin jagorancin shugaban ?asa Muhammadu Buhari ta ce ta gano tare da ?wato dala biliyan ?aya da aka sace sakamakon bincikar ku?in sata da gwamnatin ke yi tun farkon hawansa zuwa yau.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar shugaban ?asa, bayan kammala taron majalisar zartarwar ?asar da ake gudanarwa mako-mako, wanda shugaban ?asar Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Malami ya tabbatar da cewa ?udin da aka ?wato an zuba su a fannoni daban-daban na tattalin arzikin ?asar cikin har da shiri gwamnati ?asar na ya?i da talauci.

Haka kuma ministan ya bayyana damuwar gwamnati kan cushe a kasafin ?udin ?asar, ya ce hakan abin takaici ne, ya kuma ?ara da cewa za a ?auki ?wa??waran mataki domin magance hakan

Related posts

Leave a Comment