Hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS tace ta banka?o wani shiri da wasu manya a ?asar nan suke yi na ganin sun tarwatsa Najeriya.
A cikin wata takarda da jami’in hulda da jama’a na Hukumar Peter Afunanya ya sanya wa hannu kuma aka rarraba ta ga manema labarai, yace sun gano shirin manyan ne na ?o?arin jefa gaba ta ?abilanci da bambancin addini tsakanin jama’ar Najeriya, domin cimma manufar su ta tarwatsa ?asar baki daya.
Rundunar ta ?ara da cewar ‘yan sandan farin kaya da sauran ?wararru na rundunar na iya bakin kokarin su domin ganin ha?ar mutanen bata kai ga ruwa ba.
“Lallai bayanan sirri sun zo mana akan aniyar wa?annan mutane da wa?anda ke ?aukar nauyin su akan aika-aikar ta su, kuma ko ka?an hukumar mu ba zata lamunci duk wani shiri da zai haifar da rudani gami da kawo tashin hankali a Najeriya ba.
Sanarwar ta bu?aci jama’ar Najeriya masu kishi da su taimaka wa hukumar tasu da bayanai na sirri da kai rahoton dukkanin wani gungun jama’ar da basu amince da su ba.
