Mulkin Buhari Ya Jefa Arewa Cikin Matsalar Tsaro Da Ba A Taba Gani Ba A Tarihi – Baba Ahmed

An bayyana cewar yankin Arewacin Najeriya bai taba shiga halin ?a?a-ni-kayi ta fuskar matsalar tsaro a tarihi ba kamar yadda yankin ya tsinci kanshi a karkashin mulkin Buhari.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Sakataren ?ungiyar Dattawan Arewa Dr Hakeem Baba Ahmed a yayin tattaunawar da gidan talabijin na Liberty yayi dashi cikin shirin “Ina Dalili”.

Hakeem Baba Ahmed ya cigaba da cewar gwamnatin APC a karkashin jagorancin Buhari ta gaza ta kowane fanni, musanman a fannin samar da tsaro, inda yankin Arewa ya zama yanki mafi muni a koma baya a dukkanin fadin kasar.

A gefe guda Dattijon na Arewa ya koka dangane da yadda dukkanin jam’iyyun siyasa musanman manyan Jam’iyyun Siyasa na APC da PDP suka mayar da hankali akan yadda za su samu mulki kawai a 2023 ba batun halin da ?asa ke ciki ba.

Dr Hakeem Baba ya kuma bayyana cewar har yanzu jam’iyyar adawa ta PDP ba ta dauko hanya ta samun nasarar zabe ba a Najeriya, domin duk da halin da ake ciki ta gaza wajen bayyana matakan da za ta dauka na warware matsalolin Najeriya, sai han?oron kwace mulki daga APC kawai.

Related posts

Leave a Comment