Miliyoyin Yara Na Fuskantar Yunwa A Kasar Habasha – UNICEF

Asusun kula da ?ananan yara na Majalisar ?inkin Duniya ya ce mummunan fari da ba ta?a gani ba cikin gomma shekaru ya jefa miliyoyon yara cikin matsalar rashin abinci da ruwan sha a ?asar Habasha wato Ethiopia.

A wani sa?o da UNICEF ?in ya wallafa a shafinsa Tuwita ya ce da yawa daga cikin yaran na cikin hatsarin mutuwa sakamakon cutar cutar Tamowa.

Yankin gabashin Afirka na fama da mummnan farin da ba a ta?a gani ba cikin gwamman shekaru, bayan da aka kwashe damina biyar ba tare da samun girbe amfanin gona ba.

Lamarin da ya shafi mutane da dama tare da asarar dabbobi masu yawa, sakamakon rashin abinci da ruwan sha.

Related posts

Leave a Comment