Mawallafin Jaridar Lerdership Sam Nda-Isiah Ya Mutu

Allah ya yi wa mawallafin Jaridar Leadership, Mista Sam Nda-Isiah rasuwa yana da shekaru 58 a duniya.

Majiyoyi sun bayyana wa The Nation cewa marigayin ya rasu misalin ?arfe 10 na daren ranar Juma’a bayan ya koka kan cewa baya jin da?in jikinsa.

Nda-Isiah ya hallarci taron kungiyar masu jaridu ta Najeriya, NPAN, a jihar Legas a ?arshen mako.

Marigayin wanda haifaffen jihar Niger ne ya yi karatun digiri a fannin kimiyyar magunguna a Jami’ar Ife.

Ya kuma ta?a neman tikitin takarar kujerar shugabancin ?asa a jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

Wani daga cikin iyalansa ya shaidawa wakilin jaridar Punch a wayar tarho cewa:

“Eh, da gaske ne. Yanzu aka sanar da ni.”

A lokacin hada wannan rahoton, babu sanarwar rasuwarsa a shafin jaridar ta Leadership.

Sai dai wasu daga cikin fitattun mutane ciki har da kakakin Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya yi ta’aziyar rasuwarsa.

An haife shi a shekarar 1962 a Minna, Jihar Niger. Mista Nda Isaiah kuma yana da sarautar Kakakin Nupe a jihar Niger.

Related posts

Leave a Comment