Maulidin Nyass: Okorocha Ya Ba Zakiru Kyautar Mota

Sanata Rochas ya bada kyautar Mota ga wani Zakiru a yayin da ya halarci Mauludin Shehu Tijjani da Shehu Nyassa a Garin Bauchi

Sanata Rochas Okorocha ya bada kyautar mota ga Zakirun mai suna Muhammad Naziru dake cikin garin Bauchi a yayin da yake rera karatun Diwani, duk da yake Rochas ya ce ba ya fahimtar abinda ake
fada, amma shi ya ji dadi a ransa.

Daga baya kwamitin gudanar da Mauludin Sheikh Ibrahim Niasse ta girmama shi da lambar yabo.

Jama’a dai na cigaba da bayyana ra’ayoyin su akan wannan kyauta da ?an siyasar ya yi, inda wasu ke ganin hasken musulunci ne Allah ya sanya a zuciyarsa, yayin da wasu ke kallon siyasa ce kawai.

An ruwaito cewa jagoran Zikirin na jihar Bauchi Shehin ?arikar Tijjaniya Sheikh ?ahiru Bauchi ya yi addu’a ta musamman ga Rochas Okorocha din, inda ya yi addu’ar Allah Albarkaci Najeriya da ire-iren sa.

Related posts

Leave a Comment