Kungiyar Amnesty International ta ce sace fiye da ?an gudun hijira a jihar Borno da ?alibai ?ari biyu da tamanin da bakwai da malamai a yankin Kuriga a jihar Kaduna na nuna gazawar hukumomin Najeriya na kare al’umma daga hare-haren ?an bindiga da suka kashe dubban ?an ?asar cikin shekara biyar da ta gabata.
?ungiyar, cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a ta hannun shugabanta a Najeriya, Isa Sanusi, ta bu?aci gwamnatin Najeriya ta yi duk mai yiwuwa domin ku?utar da mutanen da aka sace domin ha?a su da iyalansu.
A cewar ?ungiyar, dole ne hukumomi su gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan yawaitar sace-sacen da ake yi a sassa da dama na Najeriya tare da gabatar da sakamakon binciken ga al’umma sannan su tabbatar an hukunta wa?anda aka samu da hannu a garkuwa da mutane.
Amnesty ta ce, “sace-sacen mutane da dama a baya-bayan nan ?arara sun nuna cewa shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa ba su da tsayayyen tsari na kawo ?arshen miyagun laifukan ?an bindiga da ke cin karensu babu babbaka a sassan jihohin Najeriya. Duk matakan tsaron da shugaba Tinubu da gwamnatinsa ke aiwatarwa ba sa tasiri,” in ji Isa Sanusi.
“Ganin yadda matsalar tsaro ke ?aruwa a Najeriya a yanzu, a bayyane take cewa batun kare rayuwa da dukiyoyin al’umma ya na ?asa cikin jerin abubuwan da gwamnati ta sa a gaba. Bai kamata a ?yale mutane su zauna cikin fargaba da tsoron hari da garkuwa ba.
Yawan gazawar hukumomin Najeriya wajen kare mutane abu ne da ba za a ta?a amincewa da shi ba kuma dole ne a kawo ?arshen sa,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Amnesty ta kuma yi kira da a tabbatar da wa?anda ke da nauyin samar da tsaro a yankunan da aka yi sace-sacen jama’a su yi bayani kan gazawar da ta jefa rayuwar ?aruruwan mutane cikin ha?ari.
A ranar Alhamis ne wasu ?an bindiga suka kai hari kan wata makarantar Firamare a Kuriga da ke jihar Kaduna inda suka sace ?alibai kimanin 287 da malaminsu guda ?aya, sai dai malamin ya samu ku?uta sai kuma ?alibi guda da ya mutu.
