Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce za ta mayar da rumfunan zabe 357, PUs, zuwa wuraren da babu tsaro saboda kalubalen tsaro a jihar Katsina.
A cewar hukumar, ta dauki matakin ne domin bai waduk ‘yan gudun hijira, da ke jihar damar ka?a kuri’unsu a zaben 2023.
Kwamishinan za?e na jihar, Farfesa Ibrahim Yahaya Makarfi ne ya bayyana haka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a yau Juma’a a Katsina.
Ya bayyana cewa, dokar zabe ta 2022 ta yi tanadin tsare-tsare a bayyane da kuma bayyana yadda za a gudanar da zabe a cikin yanayi na rashin tsaro.
“Sashe na 24 na dokar zabe ta 2022 ya yi tanadi ga hukumar ta yadda na za a tauye wa wani ?an gudun hijira ?ancinsu na zabe ba.
“Saboda haka, za mu tabbatar da cewa gwargwadon abin da ya dace, za mu bai wa duk wani wanda ya cancanci kada kuri’a damar yin amfani da ?ancinsa kamar yadda doka ta tanada.
