Matsalar Tsaro: Buhari Ya Fusata Da Shugabannin Tsaro

Rahotanni daga fadar Shugaban ?asa na bayyana cewar Mai girma Shugaban ?asa Buhari ya nuna fusatar shi da rashin jin dadinsa a kan rashin ?wazo da karkashin Shugabannin rundunonin tsaron ?asa.

Mai ba Shugaban ?asa shawara a kan harkokin tsaro Janar Babagana Monguno mai ritaya, ya ce Buhari ya farfa?o shugabannin rundunonin tsaron a kan bukatar su kara dagewa wajen ganin bayan ta’addanci da ayyukan ‘yan ta’adda a Najeriya.

Janar Monguno ya ce Buhari ya umarci ofishinsa ya gana da gwamnonin yankin arewa maso yamma da na maso gabas, domin ?ara nemo hanyoyin magance matsalolin tsaron, lallai Shugaba Buhari ya na cikin damuwa saboda ta?ar?arewar harkar tsaro a Nijeriya.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaron ya sanar da hakan ne a yayin tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Laraba.

Buhari ya garga?i shugabannin rundunonin tsaron da cewar su ?ara tashi haikan, su ninka kokarinsu ninkin ba ninkin na fatattakar ‘yan ta’adda a Najeriya.

A cewar Monguno, duk da shugaba Buhari ya ce shugannin rundunonin su na kokari amma kokarin nasu ya yi kadan wajen fuskantar kalubalen tsaro da kasa ke fuskanta.

Shugaba Buhari ya ce daga yanzu ba zai Kara karbar wani uzuri ba, kuma yana so su sauke nauyin da aka dora bisa wuyansu.

Monguno ya bayyana cewa shugaba Buhari ya nuna rashin jin dadinsa a kan karancin hadin kai tsakanin rundunonin tsaron, domin yin aiki tare a tsakanin hukumomin tsaron Najeriya zai taimaka wajen warware matsalar tsaro.

Related posts

Leave a Comment