Matasa Miliyan Biyar Ke Neman Shiga Shirin N-Power – Minista

Ma’aikatar Harkokin Agaji da Jin?ai ta bayyana cewa jimillar matasa 5,042,001 ne su ka yi rajistar shiga kashi na uku (Batch C) na shirin tallafi na N-Power.

An rufe rajistar shiga shirin ne a ranar Lahadi da ta gabata, wato 9 ga Agusta, 2020.

Rajistar, wadda aka fara ta a ranar 26 ga Yuni, 2020, an so kammala ta ne a ranar 26 ga Yuli amma sai ma’aikatar ta ?ara mako biyu don a bai wa wa?anda ba su yi rajistar ba damar shiga.

Ministar Harkojin Agaji da Jin?ai, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa za a bi dukkan matakan da su ka kamata don tabbatar da cewa sai wanda ya cancanta ne za a za?a domin cin moriyar shirin.

A cikin sanarwar da mai taimaka wa ministar kan harkar ya?a labarai, Halima Oyekade, ta raba wa manema labarai a ranar Litinin, an bayyana cewa ma’aikatar za ta tabbatar da cewa za a ri?a sanar da wa?anda su ka yi rajistar da ma sauran jama’a dukkan halin da ake ciki game da shirin.

Hajiya Sadiya ta ?ara da cewa manufar shirin na N-Power shi ne a ba wa matasa damar samun horo na samun aiki ko sana’a wanda hakan zai taimaka sosai wajen gina tattalin arzikin ?asar nan bayan annobar korona, wato Covid-19.

A cewar ta, za a ba mata da na?asassu fifiko a wajen za?ar wa?anda su ka yi rajistar.

Sadiya Umar Farouq ta ce ma’aikatar ta ta sadaukar da kan ta wajen ganin an cimma burin Shugaba Muhammadu Buhari na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ?angin fatara a cikin shekara 10, kuma ta lura da cewa shirin N-power na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen cimma wannan ?udirin.

Related posts

Leave a Comment