Matakan Warware Toshe Layukan Waya – Masana

Abin da ya dace ka yi idan aka dakatar da layinka bayan ka hada shi da katinka na dan kasa.

Babban jami’in sadarwa Muhammad Abdulmalik ya ce akwai mafita ga dukkan wadanda wannan matakin ya shafa, kuma na farko shi ne ya ziyarci ofishin kamfanin sadarwar da ya sayar masa da layinsa.

Ya kuma ce kamfanonin sadarwa ba sa son dakatar da layukan wayarsu, saboda yana shafar ribar da suke samu.

Kuma ya ce kamfanonin na bukatar karin abokan hulda ne ba raguwarsu ba.

Murtala Mohammed shi ne shugaban reshen hukumar da ke rajistar dan kasa a ofishinta na Masallacin Murtala a Kano ya tabbatar da wannan shawarar da babban jami’in sadarwan ya bayar.

Related posts

Leave a Comment