Rahotanni daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar Tsohon shugaban ?asa Olusegun Obasanjo ya ce makiyan ?asar da ke fatan ganin kasar ta ruguje ba za su yi nasara ba.
A wata sanarwa da kakakinsa Kehinde Akinyemi ya fitar, tsohon shugaban ya ce kasancewa dunkulalliyar kasa ya fi riba kan raba kawunanta.
Obasanjo ya shaida hakan ne a lokacin kaddamar da wani littafi a Legas.
Tsohon shugaban ya kuma kara da cewa shi masoyin Najeriya ne kuma yana sane da halin da kasar ke ciki.
Sai dai ya ce yana da ya?inin ma?iyan Najeriya ba za su kai labari ba, domin ?asar za ta ci gaba da samun wanzuwa.
