Mamman Daura Dattijo Ne Da Babu Kamarsa A Najeriya – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Malam Mamman Daura murna a ranar da ya cika shekaru 81 da haihuwa, har yake cewa “Mutane da dama suna yi wa babban dan jaridar mummunar fassara.”

Malam Daura ?an wan Buhari ne kuma babban dan kungiyar Kaduna Mafia ne, taron manyan ‘yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati, masu fasaha da kuma manyan sojojin arewacin Najeriya.

Shugaba Buhari ya bayyana cewar “Mamman Daura yana fuskantar kalubale, saboda duk wani babban mutum ba a yaba wa kokarinsa, hasali ma caccakar jama’a tana bin jijiyoyinsa.”

Shugaban kasar ya ce, “Ba zai yiwu mutum ya zauna tare da Mamman ba, bai karu da ilimi, fasaha da gogewarsa ba.” Shugaban kasar ya ce “cikin halayen Mamman da mutane ba su yaba wa sune saukin kansa, hakuri da jajircewarsa wurin taimakon na kusa da na nesa da shi. “

A yau da kake cika shekaru 81 a duniya, ina fatan Allah ya azurta ka da lafiya da tsawon kwana yayin taimakon Najeriya da al’umma, kai Dattijo ne da ire-iren ku ke wahalar samu a Najeriya.

Related posts

Leave a Comment